in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi kiran da a karfafa hadin gwiwa don kawo karshen talauci a duniya
2016-07-18 09:35:13 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa da su kara zurfafa hadin gwiwa a bangaren cinikayya da harkokin raya kasa a kokarin da ake na ganin an kawar da talauci a duniya.

Ban Ki-moon wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron harkokin cinikayya da raya kasa na MDD karo na 14 (UNCTAD) wanda aka bude a Nairobi, babban kasar Kenya, ya ce, harkokin cinikayya da zuba jari za su taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar al'umma.

Taron na tsawon mako guda, wanda ya hallara sama da wakilai 7,000 daga kasashe mambobin MDD zai tattauna hanyoyin tabbatar da dorewar shirye-shiryen ci gaba da aka tsara.

Mr Ban ya kuma koka dangane da gibin da ke karuwa tsakanin masu akwai da marasa shi a cikin al'umma. Ya kuma nanata cewa, wajibi ne harkokin cinikayya ya samar da wata makoma mai haske tsakanin al'umma da kuma duniyar da muke ciki kan hanyoyin da za su taimaka wajen tunkarar matsalar canjin yanayin da ake fuskata a halin yanzu.

Taron na UNCTAD zai kunshi dandalin kula da harkokin zuba jari na duniya, dandalin kula da harkokin kayayyaki na duniya, dandalin kungiyoyin fararen hula da kuma dandalin matasa.

Kasar Kenya ce dai ta farko cikin kasashe masu tasowa da ta samu damar karbar bakuncin taron har sau biyu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China