Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya zanta da shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma a birnin New York na kasar Amurka, game da harkokin wanzar da zaman lafiya, da sauyin yanayi da tsaro a nahiyar Afirka.
Da yake karin haske game da hakan, kakakin MDDr Stephane Dujarric, ya ce, yayin zantawar ta su, Ban Ki-moon ya jinjinawa Afirka ta Kudu bisa namijin kokari da take yi, wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar.
Kaza lika ya yi kira ga mahukuntan kasar da su rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi cikin hanzari, tare kuma da mai da hankali ga batutuwan 'yan ci rani, da masu gudun hijira, cikin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya.
A daya bangaren kuma jami'an biyu, sun jaddada muhimmancin hawa teburin shawara game da yanayin da ake ciki a kasashen Sudan ta Kudu, da Burundi da janhuriyar dimokaradiyyar Congo.
Shugaba Zuma dai ya isa birnin New York ne domin halartar babban taron MDD, wanda za a bude a gobe Talata a helkwatar majalissar.(Saminu)