in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Ba jinya shugaba Buhari ya je Jamus ba
2016-10-17 10:03:32 cri

Gwamnan jihar Imo dake kudancin Najeriya Rochas Okorocha, ya musanta rade-radin da wasu ke yi cewa, shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya ziyarci Jamus ne domin jinyar wata larura dake damun sa. Gwamnan ya ce, ko alama ziyarar da shugaban Najeriyar ya gudanar a Jamus ba ta da wata alaka da ganin likita.

Gwanman wanda ke cikin 'yan tawagar shugaban kasar yayin ziyarar aikin ta kwanaki uku, ya bayyana wa wata kafar labarai a birnin Abuja cewa, bayan dukkanin ayyukan da aka tsara yayin ziyarar, babu wata sabga da shugaba Buharin ya gudanar, illa dai ya ziyarci wani jami'in soji dake jinya a wani asibiti dake kasar ta Jamus, a hanyar sa ta zuwa filin jirgin saman birnin Berlin, kafin tashi daga birnin zuwa gida Najeriya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China