in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da tattaunawa da 'yan Boko Haram don sako ragowar 'yan matan Chibok
2016-10-17 09:41:48 cri

Ministan watsa labarai da al'adun Najeriya Lai Mohammed, ya ce mahukuntan kasar na ci gaba da daukar matakan da suka wajaba, na tattaunawa da mayakan Boko Haram, don tabbatar da cewa sun sako sauran 'yan matan nan na Chibok da suke garkuwa da su.

Mr. Lai ya bayyana hakan ne yayin wani taron addu'o'i da aka gudanar a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, domin murnar sakin 21 daga 'yan matan. Ya ce, sakin rukunin 'yan matan na wannan karo, tamkar share fage ne ga shirin da ake yi na ceto sauran yaran.

Lai Mohammed ya kara da cewa, akwai kyakkyawan fatan za a samu nasarar ceto daukacin wadanda ke tsare a maboyar mayakan kungiyar, don haka ya ja hankalin masu cece-kuce game da lamarin da su kaucewa furta kalamai, wadanda ka iya gurgunta yunkurin da gwamnati ke yi na cimma nasarar hakan.

Ministan dai ya kafe kai da fata cewa, ba musanyar fursunoni aka yi da mayakan kungiyar ba, kuma gwamnati ba ta biya wani kudin fansa ba.

Kalaman ministan dai na zuwa ne kwana guda, bayan da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da tattaunawa da mayakan kungiyar ta Boko Haram, domin cimma nasarar ceto daukacin wadanda suke garkuwa da su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China