Gwamnatin kasar Togo ta karfafa matakan tsaronta a kusantowar zaman taron gaggawa na shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Afrika (AU) kan tsaron teku da ci gban Afrika, da aka tsai da shiryawa a farkon watanni uku na shekarar 2016.
Hukumomin Togo sun karfafa binciken dare a cikin unguwanni da tabbatar da tsaro a kewayen otel otel da wuraren jama'a.
Haka kuma, an bukaci taimako da kwarewar wasu manyan kamfanonin tsaro biyu dake wannan kasa, wato kamfanin Inter-Con Security, daya daga cikin kamfanonin dake manyan kwangiloli a kasar Togo dake kuma kula da tsaro a ofishin jakadan Amurka a Togo, da kuma kamfanin GSPS Togo.
Baya ga tsaro, magajin garin birnin Lome da hukumomin ma'aikatar dake kula da harkokin teku su ma sun dauki matakai domin tsaftace hanyoyin da wuraren shakatawa na bakin ruwa. Kamar yadda aka tsai da shirya shi a ranar 4 zuwa 7 ga watan Nuwamban shekarar 2015 a Lome, an gusar da shi bisa wasu dalilai na jinkirin lokaci da aka gano wajen sake gyaren ginin otel, wanda zai karbi ayyukan wannan dandali, tare da kuma da shiryawa da kyau domin cimma burin da aka sanya gaba, in ji taron ministoci na watan Satumban da ya gabata. (Maman Ada)