Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya ce, kasarsa za ta ba da kudaden jari da ya kamata ta saka a cikin bankin kasashen dake cikin kungiyar BRICS.
A yayin da yake jawabi a Afrrica ta Kudu, shugaban ya ce, kudin da kasar za ta fara zubawa a bankin ya kai dalar Amurka miliyan 150.
Bankin na kasashen dake cikin kungiyar ta BRICS, an ba shi iznin mallakar jarin dalar Amurka biliyan dari, kuma kasashen tuni suka sanya hannu a kan alkawarin biyan dalar biliyan 50.
A taron koli na kungiyar ta BRICS a Brazil, a farkon wannan watan, kasashen dake cikin kungiyar sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya ta kafa sabon bankin raya kasa, da zimmar samar da kudade, na gina ababen inganta rayuwa, da kuma gudanar da ayyukan raya kasa masu dorewa a kasashen dake karkashin kungiyar ta BRICS, da kuma kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da kuma taimakawa tattalin arzikin kasashe masu tasowa.
Bankin na BRICS zai fi mai da hankali a fannin bunkasa makamashi, hanyar dogo da hanyar motoci, da sauran ababe na bunkasa tattalin arziki. (Suwaiba)