Mahukuntan kasar Masar sun musanta zargin da ake yi musu na tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Habasha ko kuma wata kasa.
Wadannan kalamai da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, suna zuwa ne bayan da a makon da ya gabata ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha ta gayyaci jakadan kasar Masar dake kasar domin su tattauna da shi game da wani hoton bidiyo da ke wadari a shafin intanet, inda ake nuna wani Bamisire tare wasu mambobin 'yan tawayen OLF da aka haramta a kasar a kan wani dandamali
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar Ahmed Abu Zeid ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, ganawar jami'an bangarorin biyu ta haifar da fahimtar juna game da bukatar karfafa danganta tsakanin kasashen biyu.
Kakakin ya ce, wadanda suke neman kawo baraka tsakanin kasashen biyu ne suke watsa hoton bidiyon.
Kungiyar OLF dai, kungiya ce da al'ummar yankin Oroma, kana kabila mafi girma a kasar Habasha suka kafa a shekarar 1973 da nufin kare martabar al'ummar ta Oromo. Sai dai kuma gwamnatin kasar Habasha ta ayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta'addanci.(Ibrahim)