in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu a hadarin kwale-kwalen Masar ya karu zuwa 202
2016-09-28 09:17:10 cri

Rahotanni daga kasar Masar na cewa, yawan mutuwan da suka mutu a kwale-kwalen nan da ya nutse da bakin haure a lardin Behaira da ke gabar ruwan arewacin kasar Masar ya karu zuwa 202, bayan da a jiya Talata mahukuntan kasar suka tsamo tarkacen kwale-kwalen da karin wasu gawarwaki 26 makale a cikinsa.

Sai dai kuma kamfanin dillancin labarai na kasar ta Masar Wato MENA a takaice, ya sanar da cewa, an yi nasarar ceto mutane 164 daga cikin kwale-kwalen.

A wani jawabi da ya gabatar a baya-bayan nan, shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar, ya bukaci Misirawa da hukumomin da suka dace, da su hada karfi da karfe don magance matsalar kaurar jama'a ba bisa ka'ida ba. Ya kuma ba da umarnin daukar tsauraran matakan tsaro da hukunci mai tsanani kan duk wanda aka kama da safarar mutane, a wani mataki na rage kaurar jama'a ba bisa doka ba.

Nan ba dadewa ba majalisar dokokin kasar Masar za ta sanya hannu kan dokar yaki da kaurar jama'a ba bisa doka ba wanda tuni gwamnati ta mika mata.

A makon da ya gabata ne dai kwale-kwalen dauke da daruruwan bakin haure a kan hanyarsu ta zuwa kasar Italiya ya nutse a gabar ruwan Rosetta dake lardin Behaira na arewacin kasar Masar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China