in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram 10
2016-06-12 13:03:39 cri

A jiya Asabar rundunar sojin Najeriya ta ba da sanarawar cewar, ta yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram 10 a lokacin wani samame da ta gudanar a yankin Gamboru-Ngala dake jihar Borno.

Kanal Sani Usman, mai rikon mukamin daraktan sashen hulda da jama'a na rundunar sojin kasar ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Usman ya kara da cewar, rundunar ta yi nasarar cafke mayakan na Boko Haram 2 da ransu a lokacin samamen.

A cewarsa, rundunar ta kwato makamai da alburusai masu yawa daga hannun mayakan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China