in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kori 'yan gudun hijirar Burundi dake zaune a Rwanda ba bisa ka'ida ba
2016-06-08 09:37:19 cri

An kori 'yan gudun hijirar kasar Burundi dake zaune a kasar Rwanda tun a watan jiya ba bisa ka'ida ba. Ministan harkokin wajen kasar Louise Mushikiwabo shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Talatar da ta gabata.

A watan Mayu, kinamnin 'yan gudun hijirar Burundin 1500 ne aka kora daga kasar ta Rwanda.

Da yake karin haske ga manema labarai a birnin Kigali, Mushikiwabo ya bayyana cewar, sallamar 'yan gudun hijirar, wani karamin al'amari ne, amma sakamakon matsalar tabarbarewar al'amurran tsaro ya sa gwamnatin kasar ta dauki batun da muhimmanci.

Mushikiwabo ya ce, batu ne mai sarkakaiya wajen tantance ainihin 'yan gudun hijirar a kasar ta Rwamnda, kuma mutanen za su iya kasancewa kalubale ta fuskar tsaro da zaman lafiyar kasar.

Yan gudun hijirar Burundi dake kasar Rwanda sun karu zuwa sama da 70,000, kuma daga cikin adadin, kimanin 50,000 ke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira na Mahama a gabashin Rwanda.

Mushikiwabo ya ce, 'yan gudun hijirar da aka sallama wadanda suka bar kayayyakinsu, za'a tattauna da hukumomin da abin ya shafa domin nazarin hanyoyin da za'a mayar musu da kayayyakin su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China