in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta hukunta jami'an kwastan dake hannu kan cin hanci
2015-12-03 10:52:06 cri

Gwamnatin Najeriya ta yi gargadi a ranar Laraba cewa, za ta ladabtar, sallama ko tusa keya gidan yari duk wasu ma'aikatan kwastan da aka tabbatar sun aikata ayyukan cin hanci da rashawa.

Babban jami'i mai sa ido a ma'aikatar kwastan ta Najeriya (NCS), Hameed Ali, ya yi wannan kashedi a cikin wani jawabi zuwa ga manyan jami'ai da ma'aikatan NCS a birnin Calabar, hedkwatar jihar Cross River dake kudancin Najeriya.

Ya zama wajibi mu nuna misali mai kyau kuma cikin kwarewa a lokacin da muke tafiyar da ayyukanmu na gwamnati, in ji mista Hameed Ali, tare da jaddada cewa, hukumarsa za ta aiwatar da matakin rashin nuna sassauci domin yakar cin hanci, dalilin wajabcin ga manyan jami'ai da ma'aikata da su yi watsi da duk wani nau'in cin hanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China