in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An soke ganawa tsakanin shugabannin Masar da Isra'ila
2016-02-15 10:09:08 cri

Kasar Masar ta soke ganawar da aka shirya tsakanin shugabanta da firaministan Isra'ila sakamakon subutar bakin da wani ministan Isra'ilan ya yi game da hadin gwiwwar tsaro tsakanin kasashen biyu, kamar yadda kafar yada labaran Isra'ilan ta tabbatar ranar Lahadi.

A makon jiya ne ministan makamashin Isra'ila Yuval Steinitz ya ce, dakarun sojin Masar sun cika kwararon zirin Gaza bisa bukatar Isra'ila.

Ministan ya gaya wa manema labarai na kasar Isra'ila cewa, harkokin tsaro tsakanin Masar da Isra'ila a ko da yaushe yana kan gaba, yana mai bayanin cewa, shugaban kasar Masar Abdel Fatah al-Sisi ya cika kwararon saboda sun bukaci.

Rahotanni daga Saudiyya da sauran kafofin watsa labarai na Larabawa da kafar watsa labarai ta Isra'ila Channel 2 ta sanar, an ce jami'an kasar Masar sun fusata game da subutar bakin Mr Steinitz, don haka suka yanke shawarar soke taron dake tafe tsakanin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaba Abdel Fatah al-Sisi a Alkahira.

Isra'ila dai ta musunta rahoton tana mai cewa, Mr Netanyahu ba ya da wani shiri na zuwa Masar a jadawalin shi.

Isra'ila da Masar dai sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a shekara ta 1979, kuma suna da dangantaka ta kusa a kan harkokin tsaro.

Zirin Gaza waje ne da sojojin Isra'ila da Masar suke hadin gwiwwa kuma yana a tsakanin kasashen biyu.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China