in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar wakilan Najeriya ta dakatar da Jibrin
2016-09-29 09:41:37 cri

A jiya Laraba ne majalisar wakilan Najeriya ta dakatar da 'dan majalisa Abdulmumin Jibrin na tsawon kwanaki 180 na zaman majalisa, bayan da 'dan majalisar ya zargi shugabanninta da kokarin yin cushe a kasafin kudin kasar na shekarar 2016.

Bugu da kari, an haramtawa dan majalisar rike duk wani irin mukami a majalisar, har zuwa karshen wa'adin wannan majalisa ko da kuwa wa'adin dakatarwar ya cika.

Majalisar wakilan ta bayyana cewa, zargin da 'dan majalisar ya yi tamkar bata sunan majalisar da kuma ka'idojinta ne.

Shi dai 'dan majalisa Jibrin tsohon shugaban kwamitin kasafin kudin majalisar, yana zargin kakakin majalisar Yakubu Dogara da wasu manyan jami'anta ne da yin cushe a kasafin kudin kasar na shekarar 2016, zargin da jami'an majalisar suka musanta. Ya kuma bukaci Dogara ya sauka daga mukaminsa domin a gudanar da bincike.

Bayanai na nuna cewa, mai yiwuwa wa'adin dakatarwar ta zarta watanni 12, tun da majalisar wakilan tana zama ne sau uku a kowane mako.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China