in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa sun fi son tafiya zuwa kasashen waje domin yawon shakatawa a lokacin hutun watan Oktoba
2016-10-03 13:25:50 cri

A lokacin hutun Oktoba wato yayin da ake bikin kafuwar kasar Sin, ana samun karuwa sosai a kasuwar yawon shakatawa a kasar. Bisa hasashen da kwalejin nazarin yawon shakatawa na kasar Sin ya yi, a hutun watan Oktoba, za a karbi mutanen kasar Sin miliyan 589 da zasu je yawon shakatawa, wanda ya karu da kashi 12 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Bisa alkaluman da aka samu a kamfanonin yawon shakatawa, Sinawa sun fi son tafiya zuwa kasashen waje don yin yawon shakatawa, suna son zuwa kasashen Thailand, Koriya ta Kudu, da Japan, kana Amurka, Rasha da Birtaniya sun kasance sabbin wuraren da Sinawa suke son zabi don yin yawon shakatawa.

Bisa kidayar da aka yi a shafin internet na Tuniu na yawon shakatawa, an ce, Thailand da Koriya ta Kudu da Japan sun kiyaye matsayinsu na kasancewa manyan wuraren da Sinawa suke fi son zuwa yawon shakatawa, wadanda kashi 70 cikin dari na mutanen da suka yi rajistar zuwa kasashen waje domin yawon shakatawa suka zabe su.

Wani ma'aikacin kamfanin Ctrip mai suna Tian Fei ya ce, game da hutun Oktoba na bana, Amurka da Rasha da Birtaniya sun zama sabbin wuraren da Sinawa suke fi son zuwa, inda yawan mutanen da suka zabe su ya karu da kashi 40 zuwa 60 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

Ya zuwa yanzu, kasashe da yankuna 57 sun bada biza kyauta ko bada biza bayan da aka sauka ga Sinawa. Bisa kididdigar da kamfanin Ctrip ya yi, yawan mutanen da suka zabi Morocco, Tunisiya, Tonga da sauran sabbin kasashen da suka bada biza kyauta ga Sinawa ya karu da kashi 300 zuwa 600 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China