Kasar Najeriya na gaggauta gyaren fuska a bangaren tashoshin ruwa domin zaburar shigar bangare mai zaman kansa a cikin tattalin arzikin kasar, in ji wani jami'in kungiyar masana'antun gwamnati (BPE).
A cikin wata sanarwa a birnin Lagos, Benjamin Dikki, darektan janar na kungiyar, ya bayyana cewa, gyaren fuska na canja fasalin tashoshin ruwa wajen tsarin zamanintarwa da karfi wajen samun sakamakon aiki mai kyau ga taimakawa bukatu da yin amfani da damammakin kasuwanci na zamani da tashoshin ruwa.
Mista Dikki ya bayyana cewa, bangaren na fama da gibin kayayyakin aiki, da kuma yadda gwamnati ta mamaye wannan bangare, rashin ci gaba, kulawa da kayayyakin aiki, da ayyukan tashoshin ruwa, kafin wannan yunkuri na gyaren fuska.
A cewarsa, tsarin aikin hukumar tashoshin Najeriya (NPA) ba ya aiki yadda ya kamata dalilin shisshigin gwamnati, takaita karfinta, yanayin aiki da ya sha bamban da dai sauransu.
A cewar darektan, ayyukan tashoshin ruwan ba su samu sakamako mai kyau ba sakamakon karuwar farashin kayayyakin da ake shigo da su, da kuma rashin karfin fitar da kayayyakin Najeriya a kasuwannin duniya. (Maman Ada)