in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kaddamar da tabaron hangen nesa mafi girma a duniya
2016-09-26 10:06:41 cri

A jiya Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga masana kimiyya, injiniyoyi da magina, yayin da kasar ta Sin ta fara amfani da tabaron hangen nesa mai aiki da na'ura mafi girma a duniya (FAST) a lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin a hukumance. Ko da yake an yi bikin kaddamarwar ce a yankin Pingtang da ke lardin Guizhou.

Shugaba Xi ya bayyana a cikin wasikar da ya aikewa tawagar masanan cewa, tabaron hangen nesan wanda aka yi masa labaki da suna "Idon kasar Sin na leko duniya" shi ne mafi girma da inganci a duniya. Kuma kasar Sin ce ke da ikon mallakar fasaharsa.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kaddamar da wannan na'ura wata babbar nasara ce ga kasar Sin a fagagen kimiyya, baya ga bunkasa harkokinta na kirkire-kirkire a fannin kimiyyar sararin samaniya.

A don haka, shugaba Xi ya yi kira ga masana kimiyya da injiyoyin da kwararrun da suka gina wannan na'ura, da su yi tattalinta yadda ya kamata, sannan ya yi musu fatan alheri a harkokin binciken da suke gudanarwa. Ya ce, yana fatan za su ba da babbar gudummawar da za ta kai ga kara gina kasar Sin a matsayin kasar da ke kan gaba a fannin kirkire-kirkire da harkokin kimiya a duniya.

Daga cikin ayyukan da wannan na'ura za ta gudanar sun hada da binciken iskar hydrogen a sararin samaniya, bibiyar na'urori da kumbon da aka harba cikin sararin samaniya da kuma harkokin sadarwa.

An fara aikin hada wannan nau'ra ce a shekarar 2011. Kana aka kammala girka allon na'urar wanda ya kai girman filayen kwallon kafa 30 a farkon watan Yuli.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China