in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje koli na Sin—Asiya da Turai karo na 5 a birnin Urumchi
2016-09-20 13:26:31 cri
A Talatar nan ne aka bude bikin baje koli na Sin—Asiya da Turai karo na 5 a birnin Urumchi na kasar Sin. Taken taron dai shi ne "yin shawarwari, ginawa da kuma cimma moriyar shirin zirin tattalin arziki na hanyar siliki cikin hadin gwiwa, da samar da damammaki da kuma makoma".

Wakilai daga kungiyoyin kasa da kasa 6, da kasashe da yankuna 57, da kuma kamfanonin kasar Sin da na ketare 2192 ne suka halarci bikin, baya ga sauran 'yan kasuwa 3500, adadin da ya kasance mafi girma cikin tarihin gudanarwar wannan biki.

Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majaliar wakilan jama'ar kasar Sin, da wasu manyan jami'an kasashen Tajikistan, Pakistan, Armenia, Belarus da kuma Khazakstan da dai sauransu, na cikin mahalarta bikin bude baje koli na Sin—Asiya da Turai karo na 5.

Bikin baje kolin Asiya da Turai taro ne na dandalin tattauna hadin gwiwar ci gaban tattalin arzikin Asiya da Turai, kuma muhimmin dandali ne na diflomaiyya ga shugabannin Sin da na kasashen Asiya da Turai, kana muhimmiyar hanya ce ta habaka hadin gwiwar ciniki tsakanin jihar Xinjiang ta kasar Sin da sauran kasashen dake kewayen yankin, hakan ya kuma nuna babban matsayi da jihar Xinjiang ke da shi a wannan fanni. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China