in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minstan kudi na Afirka ta kudu ya kadu da rahotonnin da ake yayatawa na kama shi
2016-05-18 10:16:20 cri

Ministan kudi na kasar Afirka ta kudu Pravin Gordhan ya bayyana cewa, shi da iyalansa sun kadu matuka da rahotannin baya-bayan nan da kafofin watsa labarai suke yayatawa cewa, babu makawa za a damke shi

A makon da ya gabata ne dai jaridar Sunday Times da ake wallafawa a kasar, ta ba da rahoton cewa, nan gaba kadan hukumar da ke yaki da masu aikata manyan laifuffuka ta kasar wato Hawks za ta damke Gordhan kan zargin da ake masa na baiwa hukumar masu yaki da aikata laifi ta kasa (NPA) wasu muhimman bayanan kudaden haraji na kasar a lokacin da ya ke rike da mukamin kwamishinan hukumar tattara kudaden haraji ta kasar daga shekarar 1999 zuwa 2009. Zargin da jami'in ya karyata.

Sai dai Gordhan ya ce, ya shafe sama da shekaru 45 yana bautawa jam'iyyar ANC mai mulki, da ciyar da kundin tsarin mulkin kasar da kuma gwamnatin kasar da ke bin tsarin demokiradiya gaba.

Don haka ya ce, bai ga dalilin da ya sa za a rika musguna masa shi da iyalansa. Amma ya ce, babu wanda ya fi karfin doka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China