Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya taya tawagar kasar sa da ta halarci gasar Olympic ta birnin Rio murnar samun lambobin yabo a gasar ta bana.
Afirka ta kudu dai ta lashe lambobin yabo 10, da suka hada da lambobin zinari biyu, da azurfa 6 da kuma tagulla biyu.
Shugaba zuma ya ce, Afirka ta kudu na alfahari da tawagar 'yan wasan ta, duba da yadda 'yan wasan suka sake nuna kwarewar su tsakanin sauran kasashen duniya. Kaza lika ya godewa daukacin al'ummar kasar bisa goyon baya da suka nunawa tawagar 'yan wasan.
Dan wasan tseren kasar Wayde van Niekerk ne ya fara lashe lambar zinari, bayan da ya karya matsayin bajimtar shekaru 17 da Michael Johnson ya kafa a gasar ta wannan karo.
Ita ma Caster Mokgadi Semenya, ta lashe lambar zinari ta gudun mita 800, bayan da ta kammala tseren ta cikin minti 1 da dakika 55.28, lambar da ta kasance ta 25, da Afirka ta kudun ta samu a tarihin gasar Olympic da ta halarta.(Saminu)