in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SACP ta bukaci a sauya shugabancin jam'iyyar ANC
2016-08-29 09:42:47 cri

Jam'iyyar kwaminis a Afrika ta kudu (SACP) ta yi kira a canza tsarin shugabancin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar.

SACP ta bayyana a karshen mako bayan kammala taron kwamitin tsakiyar jam'iyyar cewa, sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 3 ga watan Agusta, tamkar wata alama ce dake zaburar da jam'iyyar ANC mai mulki, kuma rashin daukar wasu kwararan matakai zai iya karawa jam'iyyar hasarar magoya bayanta.

Jam'iyyar ANC ta rasa iko ne a yankunan Pretoria, da Johannesburg da Nelson Mandela Bay metros a zabukan da aka gudanar, kuma wannan shi ne koma baya mafi girma da jam'iyyar ta taba fuskanta tun bayan da ta karbi iko a shekarar 1994, lamarin da ya kawo karshen nuna wariyar launin fata a kasar. A halin yanzu farin jinin jam'iyyar ANC mai mulki na ci gaba da raguwa a duk fadin kasar.

SACP ta kara da cewar, matukar jam'iyyar ta ANC ta ki daukar kwararan matakan shawo kan matsalolin cikin gaggawa, akwai yiwuwar za ta iya hasarar karfin fada a ji a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China