in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya nada shugabar hukumar zabe
2015-06-26 10:20:24 cri

Shugaba John Mahama na Ghana, ya nada Charlotte Osei a matsayin sabuwar shugabar hukumar zaben kasar EC.

Bisa nadin na ta, Osei za ta maye gurbin Kwadwo Afari-Gyan, wanda zai yi ritaya daga aiki cikin wannan wata na Yuni, bayan ya jagoranci hukumar ta EC tsahon kusan shekaru 20.

Wata sanarwa da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ta Ghana Julius Debrah ya sanyawa hannu a jiya Alhamis, ta bayyana amincewar shugaba Mahama da nadin sabuwar shugaban ECn.

Sanarwar ta bayyana uwar gida Osei a matsayin hazikar lauya, wadda ke da kwarewa da sanin makamar aiki, wadda kuma ta dade tana ba da gudummawa a sassan jagoranci daban daban.

Sai dai a daya hannu wasu daga magoya bayan tsagin 'yan adawar kasar na ta kiraye-kiraye ga shugaban kasar, da ya tuntubi masu ruwa da tsaki tukuna, kafin zabar wanda zai jagoranci hukumar zaben, a wani mataki na kalubalantar nadin da aka yiwa Osei. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China