Sakataren harkokin kasashen wajen Amurka John Kerry a Talatan nan ya ce, zai tafi kasar Rasha makon gobe domin ganawa da shugaban kasar Vladimir Putin a kan batun rikicin Syriya.
Kafin ganawar sa da ministan harkokin wajen Georgia, Mikheil Janelidze, Mr Kerry ya ce, a lokacin ziyarar tasa a makon gobe bayan ganawa da shugaban kasar, zai kuma gana da ministan harkokin wajen kasar Sergey Lavrov domin tattauna yadda za'a matso da shirin siyasar kasar cikin sauri, sa'an nan kuma a yi kokarin amfani da wannan dama.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Amurka John Kirby ya ce, ranar da Mr Kerry zai kai ziyarar za ta kasance bayan Talatar makon gobe, lokacin da zai dawo daga ziyarar aiki a kasar Cuba tare da shugaba Barrack Obama.
Mr Kerry dai da alamun zai tattauna har da batun yanayin da ake ciki a gabashin Ukraine, tare da aiwatar da yarjejeniyar Minsk a lokacin ziyarar ta shi a Moscow, a cewar sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ya fitar.(Fatimah)