in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta karyata zargin takaddama da Rasha
2016-03-15 10:11:57 cri

Mahukuntan kasar Syria sun ce, ko alama, babu wata takaddama tsakanin su da Rasha, wadda har za ta sanya Rashan janye dakarun sojin ta daga sassan kasar ta Syria.

Ofishin yada labarai na fadar gwamnatin Syria ne ya karyata zargi wanda kafofin 'yan adawar kasar ke yadawa. Ofishin ya kuma jaddada aniyar kasar Rasha, ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da bangaren Syria a fannin yaki da ta'addanci.

Da yake karin haske game da hakan, ministan yada labarun kasar Syria Omran al-Zoubi, ya ce sassan biyu na da kyakkyawar alaka, kuma matakin janye sojojin Rasha daga Syria, ya biyo bayan amincewar bangarorin biyu. Ya ce, sojojin Syria na samun galaba kwarai kan dakarun 'yan adawa. A daya hannun kuma, kasar na cimma manyan nasarori a fannin sulhu, inda tuni ma aka fara aiwatar da matakan tsagaita bude wuta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China