in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Putin ya ba da umarnin janye sojojin kasar sa daga Syria
2016-03-15 09:48:53 cri

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya ba da umarnin janye sojojin sama na kasar daga Syria, bayan wata ganawa da ya yi da ministan tsaron kasar sa Sergei Shoigu, da kuma ministan harkokin wajen Rashan Sergei Lavrov a jiya Litinin.

Wata sanarwa da aka fitar ta bayyana cewa, sojojin na Rasha za su fara komawa gida ne tun daga Talatar nan, matakin da shugaban Putin din ya ce an dauke shi ne da amincewar shugaban kasar Syria Bashar al-Assad. Kaza lika shugaban na Rasha ya ce, an kai ga cimma nasarar matakan sojin da kasar sa ke dauka a Syria.

Sanarwar ta kara da cewa, bayan janye sojojin saman na Rasha, wata tashar lura da jiragen sama mallakar Rashan za ta ci gaba da aiki a Syrian, domin tabbatar da ana aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta yadda ya kamata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China