A jiya Alhamis gwamnatin Najeriya ta sanar da cewar, za ta dauki matakan tabbatar da tsaro a yankin Niger Delta mai arzikin mai.
Babban kwanturolan hukumar shigi da fice na kasar Muhammad Babandede shi ne ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa da ministan dake kula da al'amurran yankin Niger Delta Usani Uguru Usani.
Babandede, ya nuna damuwa game da lalacewar jiragen ruwa da ake aikin sintiri da su a cikin kogunan yankin Niger Delta, sai dai ya bukaci a hada karfi da karfe domin shawo kan matsalar.
Ya bukaci ministan da ya tallafawa hukumar shigi da ficin, domin shawo kan matsalolin dake damun fannin shigi da fici ta ruwa don samar da jiragen ruwa don hukumar ta samu damar gudanar da ayyukan a yankunan yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)