in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da kai hari a kamfanin mai na Shell a Najeriya
2016-06-24 10:58:03 cri

Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta tabbatar da cewar, an kai hari kan kayayyakin kamfanin hakar mai na Shell a yankin Awarra dake jihar Imo kudu maso gabashin kasar.

Precious Okolobo, shi ne mai magana da yawun kamfanin na Shell, ya ce, dama an dakatar da amfani da bututun dake tura mai zuwa Awara, tun a ranar 8 wa watan nan da muke ciki, sakamakon mai da yake malala a yankin Okolo da Bonny na jihar Rivers.

Babu wata kungiya da ta yi ikirarin daukar nauyin harin, ko da yake dama dai kungiyar tsagerun yankin mai suna Niger Delta Avengers ta sha alwashin kaddamar da hare hare kan kayayyakin samar da man fetur da iskar gas na kasar dake yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China