in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu ana zaman dar dar a yammacin Saharar Afirka, in ji MDD
2016-09-08 10:10:48 cri

Rahotanni na cewa, yanzu haka ana ci gaba da zaman dar dar a yankunan dake daura da Guerguerat a yammacin Saharar Afirka, yankunan da kasar Morocco da dakarun Frente Polisario ke takaddama a kan su.

Da yake karin haske game da hakan, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce, 'yan yankin Frente Polisario sun kalubalanci hanyoyin mota da gwamnatin kasar Morocco, ta ayyana za ta gina a kudancin yankin Berm. Mr. Dujarric ya ce, duk da yunkurin da MDD ke yi na ganin an gudanar da kuri'ar raba gardama a yankin na yammacin Afirka, domin dakile tashin hankalin da ka iya barkewa, dakarun tsaron sassan biyu na ci gaba da jan tunga a wani wuri dake da nisan kusan mita 120 da juna.

Wannan yanki na Sahara dai na yankin arewa maso yammacin gabar tekun Afirka, ya kuma yi iyaka da kasahen Morocco, da Mauritania da kuma Aljeriya. Yankin ya kuma samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Sifaniya a shekarar 1976. Daga bisani ne kuma fada ya barke tsakanin tsagin Morocco da bangaren al'ummar yankin Polisario, kafin a cimma matsaya ta dakatar da bude wuta a watan Satumbar shekarar 1991.

MDD ta aike da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MINURSO, domin lura da halin da ake ciki, tare da fatan samun amincewar sassan biyu game da gudanar kuri'ar raba gardama game da yankin, idan har sassan biyu sun amince da hakan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China