in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya yi hasashen bunkasuwa da kashi 5 bisa 100 a kasashen dake kudu da Sahara
2014-10-22 10:25:17 cri

Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara zai karu da kashi 5 cikin 100 a shekarar 2014, kana kuma zai cimma kashi 5,75 cikin 100 a shekarar 2015.

A cikin wani rahoto, IMF ya bayyana cewa, kasashe masu karamin karfi za su samu bunkasuwa da a kalla kashi 7 cikin 100 a shekarar 2014 zuwa 2015. A cewar rahoton IMF kan hasashen tattalin arzikin shiyyar kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, jimillar hasashen cigaba na cikin wani halin ja da baya dalilin kwarya kwaryan munanan matsalolin da ake fuskanta a cikin wadannan kasashe. Wannan haskakawa tana tare da babbar matsala a kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo, inda aka samu adadin mace mace na fitar hankali, matsalolin zaman rayuwa, kuma annobar Ebola ta janyo mugun sakamako ga tattalin arziki, a lokacin da alfanun tattalin arziki da ya fara fitowa a wasu kasashe makwabta, in ji IMF. Darektar shiyyar Afrika ta IMF, Antoinette Sayeh, ta jaddada cewa, alkaluman karfin bunkasuwa a 'yan shekarun bayan nan a cikin shiyyar za su cigaba.

Madam Sayeh ta bayyana cewa, bunkasuwa za ta samu gidin zama ta hanyar zuba jari a cikin ababen more rayuwa, bangarorin masana'antu da cigaban noma.

Haka kuma, IMF ya nuna cewa, matsalar tsaro na cigaba da zama tarnakaki a cikin wasu kasashe, musammun ma Afrika ta Tsakiya da Sudan ta Kudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China