Yawancin kamuwa da cutar kanjamau a duniya a tsawon watanni goma sha biyu na baya bayan nan ya faru a kasashen dake kudu da hamadar Sahara, a cewar wasu alkaluman da aka fitar a ranar Laraba.
A tsawon wannan lokaci, fiye da mutane miliyan biyu suka kamu da cutar Sida, wanda ya kai adadin mutanen dake dauke da wannan cuta zuwa miliyan 35 a duniya, in ji rahoton hukumar yaki da cutar Sida na MDD (UNAIDS).
Rahoton na UNAIDS ya jaddada cewa, bisa mutane miliyan 35 dake dauke da wannan cuta, miliyan 19 ba su sani suna dauke da kwayoyin cutar ba. (Maman Ada)