in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a shigar da mata da matasa cikin harkokin ci gaban yanki kudu da Sahara
2015-12-15 10:52:01 cri

Wani sabon rahoton MDD ya gabatar da bukatar neman a shigar da mata da matasa masu yawan gaske cikin harkokin da suka shafi raya ci gaban kasashen kudu da hamadar Saharar Afrika.

Sabon rahoton na shekarar 2015, wanda aka kaddamar a ranar Litinin din nan a Addis Ababa, babban birnin Habasha, ya bayyana cewar, rashin nuna banbanci tsakanin jinsi da samar da guraben ayyukan yi su ne, kashin bayan ci gaban al'umma a yankunan.

Rahoton na MDD mai taken aiki don ci gaban dan adam, ya ja hankalin gwamnatocin kasashen, da su ba da muhimmanci wajen kirkiro da guraben ayyuka, har ma da ayyukan sa kai da dai sauran su.

Rahoton ya kara da cewar, ana samun ci gaba sosai ta hanyar ayyukan da al'umma ke gudanarwa a yankin na kudu da hamadar Saharar, a don haka rahoton ya bukaci a gaggauta kawar da duk wasu banbance banbance dake tsakanin jinsi domin ba da kowa damar shiga a dama da shi domin samar da ci gaba..(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China