in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saliyo ta tura maniyyatan kasa bayan dakatar da ita na tsawon shekaru 2
2016-09-06 10:05:13 cri

A jiya Litinin, shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya yi ban kwana da maniyyatan kasar su kimanin 800 wadanda za su tashi daga Freetown a yau Talata zuwa birnin Makka domin gudanar aikin Hajjin bana.

Koroma, ya fada cewa, kasar Saliyo za ta tura maniyyatanta ne bayan shafe tsawon shekaru biyu da dakatar da 'yan kasar zuwa aikin Hajji sakamakon barkewar cutar Ebola. Ya ce, hakan ya nuna a fili yadda kasar ta samu lafiya, kuma alamu ne dake nuna cewar, kasar a shirye take ta ci gaba da mu'amalar kasuwanci.

Shugaban ya ce, duniya ta yi amana cewa, kasar Saliyo tana mutunta addinai, don haka ya bukaci maniyyatan kasar da su kasance jakadun zaman lafiya a yayin da suke kasarsu, dama kasashen waje.

Sannan ya taya murna ga al'ummar musulmin kasar da suka samu damar sauke farali a wannan shekara, kana ya gargade su da su kiyaye dokokin kasar Saudiyya.

Shugaban kwamitin maniyyatan kasar Saliyo Alhaji Minkailu Mansaray, ya ce, akwai jami'an kiwon lafiya cikin tawagar maniyyatan kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China