in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sako jami'in diplomasiyar Saliyo da aka sace a Najeriya
2016-07-06 13:01:26 cri

Burgediya janar Nelson William, mataimakin babban kwamishinan kasar Saliyo dake Najeriya, ya samu saki daga hannun mutanen da suka sace shi, in ji Cornelius Deveaux, mataimakin ministan sadarwar Saliyo..

Mataimakin babban kwamishinan, da aka mika shi a ranar Talata da yamma ga hukumomin Najeriya, ya koma a halin yanzu ginin cibiyar babban kwamitin dake Abuja, in ji mista Deveaux a lokacin da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho.

An samu sakin jami'in diplomasiyan bayan da aka gudanar da shawarwari a asirce, in ji mista Deveaux, ba tare da ba da wani karin haske ba.

Fadar gwamnatin kasar ita ma ta shirya wani taron manema labarai domin tabbatar da wannan labarin na sakin jami'in diplomasiyan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China