in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Habasha ya jaddada niyyar karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu
2015-04-03 10:54:03 cri

Sabon jakadan kasar Sin da ke kasar Habasha, La Yifan ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin karfafa huldar dangantaka tsakanin Sin da Habasha.

Mista La Yifan dai ya gabatar da takardar wakilcinsa ga shugaban kasar Habasha Mulatu Teshome a yayin wani biki a fadar shugaban kasar dake birnin Addis Ababa, hedkwatar wannan kasa dake gabashin Afrika.

A cewar Genet Teshome, darektan harkokin shiyyar Asiya da Oceanie a ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha, jami'in diplomasiyyar Sin ya yi alkawarin aiki iyakacin karfinsa domin kara kyautata huldar dangantakar dake tsakanin Sin da Habasha.

Jakadan ya bayyana cewa, zai dukafa a duk tsawon wa'adin aiki, wajen gudanar da aikinsa domin karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, musammun ma a fannonin masana'antu da bunkasa ababen more rayuwa.

A nasa bangare, shugaban Habasha ya bayyana cewa, kasar Sin muhimmiyar kasa ce ga kasar Habasha, kuma jarin da 'yan kasar Sin ke zubawa na shiga cikin ayyuka daban daban na ci gaban ababen more rayuwa a kasar Habasha, kamar su hanyoyin mota, layin dogo, tashoshin wutar lantarki, makamashi, da ma sadarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China