in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu garkuwa da mutane sun bukaci kudin fansa kan wata Ba'amurkiya da suka kame a Najeriya
2015-02-27 09:32:25 cri

Wasu masu garkuwa da mutane dake tsare da wata mai wa'azin kirista Ba'amurkiya mai suna Rev. Phyllis Sortor, sun bukaci a ba su kudin fansa har dala 290,000 kafin su sake ta.

Rahotanni sun bayyana cewa, dattijuwar 'yar shekaru 87 da haihuwa, wadda aka kame a jihar Kogi ta kira wata mambar majami'ar da take aiki ta wayar tarho a ranar Talata, inda ta shaida ma ta bukatar wadanda ke tsare da itan.

Da yake tabbatar da aukuwar lamari, kwamishinan 'yan sandan jihar Adeyemi Ogunjemilusi, ya ce, rundunarsa na daukar dukkanin matakan da suka wajaba domin kubutar da matar.

A daya hannun kuma gwamnan jihar Kogi Idris Wada, ya yi Allah wadai da kame matar.

Wasu mutane su 6 da ba a san ko su waye ba ne dai suka sace Sortor a ranar Litinin, a harabar majami'ar da take aiki wadda ke yankin Emi Woro a jihar ta Kogi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China