in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe wani Bajamushe a kudu maso yammacin Najeriya
2014-10-28 09:55:30 cri

Wasu 'yan bindiga da ba a tantance su ba, sun harbe wani Bajamushe da ke aiki da kamfanin Julius Berger har lahari a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

A cewar kamfanin na Julius Berger, an harbe mutumin da ba a bayyana sunansa ba ne ranar Jumma'ar da ta gabata, lokacin da yake tafiya da sauran ma'aikatan kamfanin ba tare da rakiyar jami'an tsaro ba.

Bugu da kari, kamfanin ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ba ya ga wannan ma'aikacin, an kuma sace wani ma'aikanaci na daban, amma suna aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro na Najeriya don ganin an saki mutum da aka sace cikin koshin lafiya.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin aikata wannan lamari ko bukatar wani kudin fansa. Sai dai hukumomin tsaro a jihar ta Ogun sun bayyana cewa, jami'an 'yan sanda sun fara farautar 'yan bindigar da ke rike da ma'aikacin kamfanin na Julius Berger.

Batun sace mutane dai ya zama ruwan dare a Najeriya, inda aka sace sama da 'yan kasashen waje 300 a yankin Niger Delta mai arzikin mai tun a shekarar 2006, ko da yake an saki dukkan mutanen bayan da aka biya kudin fansa.

An samu karuwar aikata manyan lafiffuka a kasar da ke yammacin Afirka ne tun lokacin da kasar ta kamu ga tsarin mulkin demokirdiya a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 1999, bayan shafe shekaru 15 tana karkashin mulkin soja.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China