Rundunar 'yan sandan jihar Rives da ke kudu maso gabashin Najeriya ta tabbatar da cewa, wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon shugaban kungiyar lauyoyin jihar Okey Wali.
Kakakin rundunar 'yan sandar jihar Muhammed Ahmad ya shaidawa manema labarai a garin Fatakwal, babban birnin jihar cewa, an sace Okey Wali ne ranar Asabar ba tare da sanin inda aka kai shi ba.
Ya ce, bayanan da suka samu ya nuna cewa, sai da suka kai ruwa rana da wadanda suka yi awon gaba da shi kafin su tafi da shi.
Kakakin 'yan sandan ya shaidawa manema labarai cewa, 'yan sanda na gudanar da bincike don ganin sun kwato Wali cikin koshin lafiya. (Ibrahim)