Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ayyana cewar, ta cafke jagoran masu kaddamar da hari kan bututun man kasar wadanda ke farfasa bututun mai na NNPC da kamfanin mai na Chevron da iskar gas na kasar a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.
Kwamandan rundunar sojin ruwan kasar mai kula da jihar Delta Raimi Mohammed, ya shedawa taron manema labarai a Warri cewar, an samu nasarar damke madugun tare da sauran tsagerun dake farfasa bututun man kasar ne a ranar 2 ga watan Yuni.
Mohammed ya bayyana damke madugun a matsayin wata babbar nasara, ya kara da cewar, sun kwato wasu abubuwan fashewa masu yawa wadanda tsagerun ke amfani da su wajen farfasa bututun man.
Ya kara da cewar, wadanda ake zargin, suna fasawa tare da satar danyen man, sannan an samu nasarar damke jagoran tsagerun ne mako guda bayan kama wasu daga cikin na hannun daman madugun.
Mohammed ya ce, rundunar soijin ruwan kasar ta kama wani mutum mai suna Michael John, wanda ake zargi da hallaka wasu sojoji 3 a Jones Creek da wani soja da wani 'dan sanda a yankin Batan.
Mohammed ya tabbatar da cewar, rundunar sojin ruwan a shirye take ta kare dukkan nin kan iyakokin ruwan kasar.
Hare haren fasa bututun man a yankin Niger Delta na kara kamari a 'yan makonnin da suka gabata, kungiyar Niger Delta Avengers ta yi ikirarin alhakin kaddamar da hare haren.(Ahmad Fagam)