in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNDP ya kaddamar da shirin tallafawa Afirka wajen dakile yaduwar tsattsauran ra'ayi
2015-11-25 14:10:41 cri

Asusun samar da ci gaba na UNDP, ya kaddamar da wani sabon shirin tallafawa Afirka, wajen kandagarki, da kuma magance yaduwar tsattsauran ra'ayi tsakanin al'ummar nahiyar.

An dai kaddamar da shirin na shekaru 4 ne a ranar Talata, zai kuma lakume kudi har dalar Amurka miliyan 45 da dubu dari 7. Ana sa ran wannan shiri zai ba da damar magance dalilan dake haifar da yaduwar munanan akidu tun daga tushe.

Wata sanarwa da aka fitar game da wannan sabon shiri, ta nuna cewa, UNDP na da burin amfani da dabaru mabanbanta a kasashen daban daban, musamman game da wadanda ayyukan masu tsattsauran ra'ayi suka shafa, da masu makwaftaka da su, da ma wadanda ke fuskantar barazana daga masu tsattsauran ra'ayin.

Kaza lika sanarwar ta ce, shirin na da burin gudanar da hadin gwiwa da hukumonin kasa da kasa, da na shiyya shiyya wajen samar da goyon baya, da gano alamun tsattsauran ra'ayi tun daga matakin farko, da kuma hanyoyin kandagarkin matsalolin dake biyo bayan hakan.

Tashe-tashen hankula da masu tsattsauran ra'ayi ke haddasawa sun dade suna haifar da munanan sakamako ga zamantakewa, da tattalin arzikin al'ummun nahiyar Afirka, inda ayyukan kungiyoyi irin su Boko Haram da Al-Shabaab, suka zamo sanadiyyar raba dubban al'ummar nahiyar da gidajensu, baya ga wadanda ke rasa rayukansu a lokuta daban daban.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China