in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi tir da hari kan hedkwatar ma'aikatar ilimin Somaliya
2015-04-16 10:38:48 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya yi tir da harin da aka kai a hedkwatar ma'aikatar ilimi ta kasar Somaliya a ranar Laraba a babban birnin kasar Mogadishu, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, har da jami'an tsaron na soji.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, kwamitin ya ce, duk wani nau'in rashin hankali na ta'addanci a Somaliya ba zai dakushe aniyarsa ta marawa kasar baya ba domin ta sulhunta tare da samar da zaman lafiya.

Kungiyar Al-Shabaab dake da alaka da al-Qaida ta kasar ta dauki nauyin harin da aka kai ranar Talata kwana daya da ma'aikatar ta sanar da cewa, jarraba da jadawalin karatun, za'a fara yin su bai daya a daukacin fadin kasar.

Sojoji 6 da fararen hula 15 ne wannan hari ya rutsa da su a cikin ginin dake dauke da ma'aikatar ilimi, da ma'aikatar man fetur da ma'adinai.

Jami'an tsaron Somaliya 5 da na kungiyar AMISOM 1 suka hallaka lokacin da suka tare da wadanda za su kai harin a ginin ma'aikatar bayan da suka lalata gininta da motarsu dake makare da bama bamai, a cewar wani jami'in tsaro a wajen.

A dangane da wannan, kwamitin tsaron ya jaddada goyon bayansa ga duk wadanda ke da hannu a cikin kokarin samar da zaman lafiya a Somaliya da suka hada da AMISOM, kungiyar wanzar da zaman lafiya ta AU da hadin gwiwwar MDD a Somaliyan. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China