in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun hallaka 'yan tawaye 5 a kudancin kasar
2016-08-29 10:15:51 cri

Mahukunta a Najeriya sun ce, sojojin kasar sun hallaka 'yan tada kayar baya 5, sannan sun damke 23 a yayin wani samame a yankin Niger Delta mai arzikin mai.

A wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labaru na Xinhua a Legas, mai rikon mukamin daraktan hulda da jama'a na rundunar sojin kasar kanal Sani Usman ya bayyana cewar, dakarun runduna ta musamman ta 133 ta sojojin kasar, sun yi nasarar kwace bindigogi kirar AK-47 guda 2, da kananan bindigogi 11, da harsasai 292, da harsasan bindigar AK-47 199, da kuma injunan janareto 4 a yayin simamen a ranar Asabar.

A 'yan watannin da suka gabata ne, kungiyar 'yan tada kayar baya ta Niger Delta Avengers NDA ta kaddamar da hare hare kan bututun mai da iskar gas na kasar dake yankin Niger Delta.

Su dai 'yan tada kayar bayan suna fafutukar neman karin kudaden haraji ne daga kamfanonin dake hako man fetur a yankin, da neman a sako 'yayan kungiyar da ake tsare da su, da kuma ci gaba da biyan su kudade karkashin shirin nan na yin afuwa.

Hare haren tsagerun yankin Niger Delta sun tilasta wasu daga cikin kamfanonin hako mai na kasashen waje kauracewa yankunan. Tuni dai gwamnatin kasar ta umarci dakarun soji da jami'an tsaro a yankunan da su ci gaba da kare albarkatun man fetur dake yankunan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China