in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattijan Najeriya za ta binciki batun karkatar da abincin 'yan gudun hijira
2016-08-29 10:09:36 cri

Majalisar dattijan Najeriya ta sanar a jiya Lahadi cewa, za ta binciki halin matsananciyar yunwa da ake fama da ita a sansanonin 'yan gudun hijira dake jahohin arewa maso gabashin kasar.

Shugaban majalisar dattijan Najeriyar Bukola Saraki ya tabbatar da hakan, cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua game da yunkurin zanga zangar da daruruwan mata a sansanonin 'yan gudun hijirar dake jihar Borno suka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya bayyana halin da suka shiga a matsayin abin tausayi, kana ya bukaci gwamnati da hukumomin agaji na kasa da kasa da su kawo dauki.

Saraki ya kuma bukaci 'yan sandan Najeiya, da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC, da hukumomin shari'a da su hanzarta bincikar batun karkatar da abinci 'yan gudun hijirar.

Ya kara da cewa, jami'an gwamnati da 'yan kwangila su ne ke da alhakin batar manyan motoci makare da abinci da aka shirya kaiwa sansanonin 'yan gudun hijirar.

Saraki ya ce, da zarar majalisar ta koma bakin aiki a watan Satumba, zai gabatar da batun halin da ake ciki a yankin arewa maso gabashin kasar a zauren majalisar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China