in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da UK suna karfafa hadin gwiwa a bangarorin zaman lafiya da tsaro a Afirka
2016-06-02 10:09:19 cri

Kungiyar tarayyar Afirka da kasar Burtaniya, sun lashi takwobin karfafa hadin gwiwa don ganin an magance kalubalen tsaro da ke addamar nahiyar Afirka.

Kwamishinan zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afirka Smail Chergui, shi ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zantawa da sakataren harkokin wajen Burtaniya, kana mai kula da harkokin kasashe renon Ingila Philip Hammond.

Wata sanarwa da kungiyar ta AU ta fitar ta ce, jami'an biyu sun kuma tattauna kan ci gaba da aka samu na baya-bayan nan a kasashen Libya da Somaliya da kuma batutuwan da suka shafi yadda za a dauki nauyi kan ayyukan wanzar da zaman lafiya da AU ta ke jagoranta.

Bugu da kari, jami'an sun yi musayar ra'ayoyi game da yaki da Boko Haram, inda suka nanata kudurinsu na kara daukar matakai a yakin da ake yi da 'yan ta'addan.

Sun kuma yaba da ci gaban hadin gwiwar da ke tsakanin kungiyar AU da kasar Burtaniya. A saboda haka ne ma suka sake jaddada muhimmancin da ke akwai na kara karfafa hadin gwiwa da tsara matakai domin ganin an magance kalubalen zaman lafiya da tsaro da nahiyar ta Afirka ta ke fuskanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China