Bayan da aka tabbatar da ficewar kasar Birtaniya daga kungiyar EU a ranar 24 ga wata bisa sakamakon zaben raba gardama da aka gudanar, wakili mai kula da harkokin hada-hadar kudi na kwamitin kungiyar EU Jonathan Hill, wanda ya fito daga kasar Birtaniya ya sanar da yin murabus a jiya Asabar.
Mr. Hill ya bayyana cewa, yana sa ran kasar Birtaniya za ta kara taka rawa wajen inganta gudanar da cinikayya cikin 'yanci a nahiyar Turai, amma jama'ar Birtaniya sun tsai da kudurin ficewa daga kungiyar EU, kuma yana bakin ciki a game da sakamakon.(Lami)