Tsohon faraministan Burtaniya Tony Blair ya nemi gafara game da kuskuren aka samu wajen shirya yakin Iraki, tare da amincewa da cewa, bayanan da suka samu ba su da sahihanci, a cewar wani labarin da kafofin Burtaniya suka rawaito a ranar Lahadi.
Mista Blair ya amince cewa, akwai wasu abubuwa na gaskiya game da mamaye Iraki a shekarar 2003, da kuma suka kasance babban dalili na kafuwar kungiyar IS a halin yanzu, in ji gidan talabijin Sky na Burtaniya.
Ina neman gafara game da cewa, bayanan da muka samu na karya ne, in ji mista Blair a cikin wata hira da gidan talabajin CNN na Amurka. Ina kuma neman gafara da kuma kuskuren tsara wannan yaki, kana da hakikanin kuskurenmu na fahimtarmu kan abin da ya faru bayan mun kawar da gwamnatin Saddam Hussein, in ji Tony Blair. A cikin intabiyun, mista Blair ya amince da cewa, akwai alaka tsakanin yakin Iraki da a halin da ake ciki a kasar Iraki, musammun ma game da ci gaban kungiyar IS. (Maman Ada)