in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na nuna sha'awa ga ayyukan ginin layin dogo na kamfanonin kasar Sin
2016-02-02 10:30:09 cri
Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana sha'awar da gwamnatin sa ke da ita, game da tayin da kasar Sin ta yi na gina wasu manyan layukan dogo a Najeriya.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a kasar Habasha, lokacin da yake ganawa da 'yan kasar sa mazauna Habashan. Ya ce tuni ya baiwa ministocin ma'aikatun sufuri, da na kudi, da na makamashi, ayyuka da gidaje, umarni na duba hanyoyin sake tattaunawa da mahukuntan kasar Sin, domin cin gajiyar tallafin kasar ta Sin a wannan fanni.

Kaza lika shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa na nazarin yarjeniyoyin ayyukan ginin layin dogo, wadanda ta gada daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata da nufin farfado da su. Ya ce a baya gwamnatin kasar Sin ta amince ta samar da kaso 85 bisa dari, na kudaden gudanar da wasu manyan ayyukan ginin layin dogo, sai dai ba'a cimma nasarar gudanar su ba, sakamakon gazawar da Najeriya ta yi na samar da kaso 15 da ta yi alkawari.

A wani ci gaban kuma, jakadan Sin dake Najeriya Gu Xiaojie, ya gana da ministar ma'aikatar kudi Kemi Adeosun, da na sufuri Rotimi Amaechi, a birnin Abuja, domin lalubo karin hanyoyin bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya, a fannin zuba jari da hada-hadar kasuwanci.

Yayin zantawar ta su, jakada Gu ya ce wannan shekara ita ce ta cikon 45 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin sassan biyu. Kana kasar Sin na fatan daukar karin matakai na fadada alakar ta da Najeriya a dukkanin fannonin ci gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China