in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya tattauna tare da John Kerry kan ta'addanci da tattalin arziki
2016-08-24 11:17:48 cri

A jiya Talata ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tattauna da John Kerry, sakataren harkokin wajen kasar Amurka da ke ziyarar aiki a kasar, kan wasu batutuwan da suka hada da kokarin yaki da ta'addanci, tattalin arziki, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Wata sanarwa ta fadar shugaban kasar Najeriya ta nuna cewa, Mista Kerry ya kuma tattauna tare da shugaba Buhari kan wasu muhimman kalubale na cikin gida, da na shiyya shiyya da suka hada da boren kungiyar Boko Haram, da kuma halin da al'ummomin da suke kaura daga muhallinsu dalilin rikicin na Boko Haram ke ciki.

A yayin ziyararsa a Abuja, mista Kerry zai gana da wani gungun gwamnonin jihohin arewacin Najeriya. (Laouali Souleymane).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China