Dakarun Najeriya da ke yaki da mayakan Boko Haram za su kara zafafa hare-haren da suka kaiwa a tungar mayakan dake dajin Sambisa, a wani mataki na ganin an kakkabe gyauron kungiyar.
Babban hafson tsaro na Najeriya janar Gabriel Olanisakin wanda ya bayyana hakan ga manema labarai, ya ce, matakan kakkabe mayakan na Boko Haram na baya-bayan nan da aka kaddamar a dajin na Sambisa, ya fara haifar da kyakkyawan sakamako, ciki har da 'yan makarantar sakandaren Chibok guda biyu da aka ceto.
Olanisakin ya ce, ana ci gaba da kaddamar da kai hare-hare a dajin na Sambisa wanda aka yi imanin cewa, shi ne ragowar tungan 'yan ta'addan. Ya kuma bayyana cewa, yanzu haka an karya lagon kungiyar, ta yadda ba za iya kai wasu hare-hare kamar yadda ta saba yi a baya ba.
Kungiyar Boko Haram dai ta halaka sama da mutane 10,000, galibinsu a yankin arewa maso gabashin kasar, tun lokacin da ta fara kaddamar da hare-hare a shekarar 2009. Ta kuma sace sama da 'yan mata 200 daga makarantunsu a garin Chibok. Yanzu haka akwai 'yan mata 217 da ba a san inda suke ba.
Sai dai a shekarar da ta gabata dakarun kasar sun sake kwato wasu garuruwa da ke karkashin ikon kungiyar a can baya.(Ibrahim)