Jami'an shirya gasar sun tabbatar da hakan a Juma'ar data gabata, inda suka ce an fitar da kungiyar 'yan wasan kwallon kafan kasar Zambiyan ne, bayan wani gwaji da aka gudanar, inda sakamakon gwajin ya nuna cewar biyu daga cikin 'yan wasan kasar shekarunsu sun zarta 17.
Kasar Zambiya ta mika 'yan wasan gabanta biyu wato Nicholas Mulilo da Benjamin Phiri bisa radin kanta, domin sake yi musu gwaji a wasannin wanda ake gudanarwa a Mauritius, bayan korafe korafen da wasu kasashe biyu suka yi game da 'yan wasan.
Sanarwar ta bayyana cewa, an yi waje da kasar Zambiya ne, bayan sake gwajin da aka gudanar a kan Nicholas Mulilo, da Benjamin Phiri a Mauritius, bayan an gano sun dara shekaru 17 da haihuwa, wanda ya saba da sashe na 10.5 (1) na dokokin wasannin kwallon kafar hukumar.