in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magoya bayan 'yan wasan Najeriya sun jinjinawa tawagar kwallon kafar kasar
2016-08-24 13:26:09 cri
Masoya kwallon kafa a Najeriya sun jinjinawa tawagar kwallon kafar kasar 'yan kasa da shekaru 23, bisa nasarar lashe lambar tagulla da suka yi a gasar Olympic ta birnin Rio. Magoya bayan kungiyar dai sun bayyana farin cikin su, ganin tawagar Najeriyar a wannan karo bata dawo gida hannu rabbana ba.

Da yake tsokaci game da hakan, tsohon kocin kungiyar Super Eagles Christian Chukwu, ya ce kwarewar da 'yan wasan kungiyar suka nuna, da kuma biyayyar su ga masu horaswa ne ya basu damar samun nasara kan Hunduras.

Chukwu ya ce idan da 'yan wasan sun kwatanta hakan yayin wasan su da Jamus, da sun lashe lambar azurfa. Duk da hakan dai ya ce lambar tagulla ta fi dawowa gida haka nan.

Daga nan sai ya yi fatan 'yan wasan kasar za su taka rawar gani a gasar Olympic ta shekarar 2020 wadda za a gudanar a kasar Japan.

Najeriya dai ta taba lashe lambar zinari a gasar da ta gudana a shekarar 1996 a birnin Atlanta na Amurka, ta kuma lashe lambar azurfa a shekarar 2008, lokacin da aka gudanar da gasar a nan birnin Beijing.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China