in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta bukaci Afrika da ta kara kokarin rage mace macen mata da jarirai
2014-11-14 15:32:51 cri

Darektar bincike kan lafiyar aifuwa ta kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), Marleen Temmerman ta yi kira a ranar Alhamis ga kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara da su yi kokarin rage mace macen mata da jarirai ta hanyar karfafa tsare tsaren kiwon lafiya. Ya kamata gwamnatoci su yi kokarin kyautata tsare tsaren kiwon lafiyarsu, tare da samar da ingancin alkaluma, ta yadda za'a iyar yin rajistan dukkan mace macen mata da jarirai, in ji madam Temmerman a birnin Nairobi, a yayin wani taro kan gaggauta kokarin kan mace macen mata da yara kanana.

A cewar WHO, matsayin alkaluman mace macen mata da yara kanana a kasar Kenya bai canja ba sosai tsakanin shekarar 1990 da shekarar 2013, inda ya wuce daga 490 zuwa 400 a cikin haifuwa dubu dari ta yaran da suka rayuwa. Raguwar mace macen mata da yara kanana a tsawon wannan lokaci yana kasa da kashi daya cikin dari a shekara, bisa kashi 5,5 cikin 100, mizalin da aka bukata na cimma burin MDGs.

Wakilin kasar Kenya kan asusun kananan yara na MDD, Siddarth Chatterjee ya bayyana a nasa bangare cewa, kasar Kenya za ta iyar fita daga jerin kasashe goma mafi hadarin wajen haifuwa idan har ta rike kokarinta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China